An gama shari'ar matar Bo Xilai a China

Hakkin mallakar hoto
Image caption Gu Kailai

An kammala shari'ar Gu Kailai-matar fitaccen dan siyasar nan da aka daina damawa da shi a gwamnatin China, Bo Xilai bisa tuhumar laifin kisan kai a gaban wata kotu da ke birnin Hefei.

Shari'ar dai ta biyo bayan badakalar siyasar da ta kifar da mijinta ne ta kuma kawo yamutsi a jam'iyyar 'yan gurguzun da ke mulkin China.

Ana dai zargin Gu Kailai, da wani mai aikin gidan ta ne da kashe abokin kasuwancin ta dan kasar Burtaniya, Neil Heywood a wani sabani da suka yi game da kudi.

Matsayin mijin na ta a siyasar kasar ta Sin ne yasa shariar ta dada zama mahimmiya a idanun duniya.

Karin bayani