Gu Kailai ta amsa laifin kisan Neil Heywood

Neil Heywood da Gu Kailai Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Neil Heywood da Gu Kailai

Kafofin yada labarai na gwamnatin China sun ce matar sannannen dan siyasar nan Bo Xilai ta amsa cewa ita ta kashe abokin kasuwancinta dan Birtaniya Neil Heywood, a wani hali da ta kira na tabin hankali.

Al’amarin dai ya jawo rikicin siyasa a kasar wanda aka jima ba a ga irin sa ba.

A wani cikakken rahoto da ya bayar, kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya Ambato Gu Kailai tana neman afuwa saboda bala’in da ta haddasa.

Masu sharhi a kan al'amura na ganin amsa laifin nata zai iya sawa a yi mata rangwame a hukuncin da za a yanke mata.

Tun da farko ranar Juma’a jami’na kotu sun ce wasu ’yan sanda hudu sun amince cewa sun yi yunkurin rufa-rufa dangane da kisan dan kasuwar.

Karin bayani