Girgizar kasa ta hallaka mutane 180 a Iran

Wata girgizar kasa a Iran a 2005 Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wata girgizar kasa a Iran a 2005

Girgizar kasa mai karfi ta jijjiga arewa maso yammacin Iran har sau biyu ba kakkautawa.

Jamiā€™ai sun ce akalla mutane dari da tamanin sun rasa rayukansu yayin da fiye da dubu da dari uku suka jikkata.

An bayar da rahoton cewa girgizar kasar ta katse duk wadansu hanyoyin sadarwa da yankin wanda ke kusa da birnin Tabriz, al'amarin da ya sa hukumomi ke shan wahala wajen tantance barnar da ta auku.

Amma dai wani jami'i a yankin ya shaidawa BBC cewa girgizar kasar ta yi mummunar barna ga kauyuka kusan sittin.

Girgizar kasar mai karfin maki shida da digo hudu da kuma maki shida da digo uku ta haddasa daukewar wutar lantarki a galibin birnin Tabriz.

Karin bayani