Mitt Romney ya zabi Paul Ryan a matsayin mataimaki

Mitt Romney da Paul Ryan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mitt Romney (daga hagu) da Paul Ryan

Dan takarar jam'iyyar Republican a zaben shugaban kasar Amurka na bana, Mitt Romney, ya bayar da sanarwar cewa ya zabi Paul Ryan a matsayin dan takararsa na mataimakin shugaban kasa.

Paul Ryan dan majalisar dokoki ne mai ra'ayin rikau daga Wisconsin, kuma shi ne yake shugabantar kwamitin kula da kasafin kudi a Majalisar Wakilai inda 'yan jam'iyyar ta Republican ke da rinjaye.

Mista Ryan ya sha alwashin warware sauye-sauyen Shugaba Obama a harkar kiwon lafiya, yana kuma kan gaba a fafutukar ganin an rage kashe kudaden gwamnati matuka ainun.

Sai dai wani wakilin BBC ya ce ayyana sunan Paul Ryan zai kara kawo rarrabuwar kawuna a muhawarar da ake yi dangane da makomar tattalin arzikin Amurka.

Karin bayani