An bukaci kawo karshen yunwa a Afrika

Image caption Taron Kasashen Afrika

Talatin daga cikin mawaka da 'yan wasan fina-finan da suka yi fice a nahiyar Afrika, sun bukaci shugabannin da za su halarci taron yaki da yunwa a London su kawo karshen matsalar a nahiyar.

Taurarin sun bukaci taron da za'a fara a ranar lahadi da ya dauki abin da suka kira matakai na kurkusa na warware matsalar yunwar.

A wasikar da suka aikawa jaridar The Guardian ta Birtaniya, fitattun taurarin sun ce yunwa na yiwa kasashen gabashi zuwa yammacin Afrika fyadar 'ya'yan kadanya, inda fiye da mutane miliyan ashirin ke fama da ita.

A cewarsu, daukar matakai masu dogon zango ne kawai zai kawo karshen matsalar yunwa a kasashen Afrika.

Firai ministan Birtaniya David Cameron, na fatan ganin taron da za'a yi a ranar da za a kammala wasannin Olympics zai kasance daya daga cikin abubuwan da za su kafa tarihi a gasar, ta yadda kasashen duniya za su tashi tsaye wajen daukar matakan magance matsalar yunwa.

Karin bayani