An binne tsohon shugaban Ghana Atta Mills

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Marigayi Atta Mills na Ghana

A ranar Juma'a ne ake binne marigayi shugaban kasar Ghana John Atta Mills a Accra babban birnin kasar, bayan kammala makokin kwanaki uku.

Shugabannin kasashen Afrika da dama ne suka halarci jana'izar marigayin tare da sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton.

Mutuwar ba-zatan da Mr. Atta Mills ya yi makwonni biyu da suka wuce ta girgiza al'ummar Ghana kuma jerin gwanon masu bankwana da gawar sa ya kai tsahon kilomita goma.

Sakatariyar harkokin wajen Amurkar Hillary Clinton ta je Ghana ne bayan ta ziyarci Najeriya inda ta gana da shugaba Goodluck Jonathan ta kuma bukaci shugaban ya kara kaimi kan tsare tsaren ci gaban kasa yayin da kasar ke fuskantar hare-haren bamabamai.

Clinton dai za ta gana da sabon shugaban kasar ta Ghana, John Dramani Mahama, tsohon mataimakin Atta Mills wanda aka rantsar da shi ya maye gurbin tsohon shugaban 'yan sa'oi bayan mutuwar tsohon shugaban.

Ghana dai ana mata kallon wata abar kwatance kan ci gaban dimokradiyya a Afrika ta Yamma.

Shugaban kasar Amurka Barack Obama nan ya fara ziyarta a kasashen Afrika dake kudu da Sahara a lokacin da ya zama shugaban kasar a shekara ta dubu biyu da tara.

Hillary Clinton dai ana tsammanin za ta isa kasar Benin ranar Juma'a kasa ta karshe da za ta je a wannan ziyarar.

Ta dai ziyarci kasashen da suka hada da Senegal da Sudan ta kudu da Kenya da Malawi da Afrika ta kudu da kuma Najeriya.

Karin bayani