Dakarun Masar sun kama mutane tara a Sinai

dakarun Masar a yankin Sinai Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption dakarun Masar a yankin Sinai

Gidan talabijin na kasar Masar ya ce sojoji sun kama mutane tara a yankin Sinai, inda suka kara karfafa matakan tsaro.

An tsaurara matakan tsaron ne a yunkurin kawo karshen ayyukan masu fafutukar Islama da suka kafa sansanoni a wasu kauyuka dake iyakokin zirin Gaza da Ira'ila.

Rundunar Sojin Masar na ci gaba da kara jibge dakarun soji a yankin na Sinai, bayan wasu rahotani dake cewa sun kashe 'yan gwagwarmaya kimanin ashirin ranar Laraba, a matsayin ramuwar gayya kan kisan da aka yi wa sojoji goma sha shidda.

A Wata tattaunawa da Ministan harkokin cikin gida na kasar Ahmed Gamal Al-Deen yayi da shugabannin Larabawan kauye, sun amince za su ba wa sojoji da 'yan sanda hadin kai domin tabbatar da tsaro a iyakokin kasar.

Shugaban Kasar Masar, Muhammad Morsi, ya kori wasu manyan jami'an tsaron kasar, da kuma gwamnan Arewacin Sinai, a kokarin da gwamnatin ke yi na mayar da martani mai karfi a kan duk wanda ya nemi kalubalantar ikon gwamnati.

Sai dai wasu na nuna shakku kan ko daukar matakan soja, ko na korar wasu manyan jami'ai zasu yi tasiri a wannan yanki, wanda ake samun karuwar nuna kaifin kishin addini, da kuma karya doka.

Karin bayani