Majalisar Libya ta zabi shugaba

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Murna a Libya

Sabuwar zababbiyar majalisar dokokin Libya ta zabi tsohon jagoran 'yan adawa Muhammad Megar-yef a matsayin shugaba.

Mr. Megar-yef zai jagoranci majalisar wurin sauke nauyinta na nada firaminista da kuma tafiyar da kasar kafin samar da sabon tsarin mulki a badi tare da gudanar da zaben majalisa na gama-gari.

Sabon shugaban, mutum ne mai sassaucin ra'ayin addinin Islama kuma jagora ne a kungiyar 'yan adawa mafi dadewa a kasar, wacce ta kwashe shekaru da dama ta na yunkurin hambarar da gwamnatin Gaddafi.

Mr Megaryef ya yi gudun hijira na tsawon shekaru ashirin inda ya zauna a Amurka da kuma wani dan zama da ya yi a Birtaniya.

Karin bayani