An yanke hannun barawo a Mali

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mujao

Kungiyar yan kishin Islamar dake iko da arewacin kasar Mali ta yanke hannun wani mutum a matsayin haddi na yin sata.

Kakakin kungiyar ya ce an aiwatar da hukuncin ne a bainar jama'a.

Haka nan ya kuma yi gargadin cewar za a aiwatar da irin wannan hukunci a garin Gao, inda masu zanga-zanga suka nuna bijirewa ga hukucin yanke hannun a karshen makon da ya gabata.

A makon da ya gabata, kungiyar Ansarudeen ta yi wa wasu mazinata da suka taba yin aure rajamu a garin Aguelhok.

Kungiyar ta kuma rugurguza wajajen bauta masu dadadden tarihi ta kuma yi Allah wadai da bunkasar abinda ta kira bautar gumaka.

Gwamnatin wucin gadin Mali ta bayana cewa guntule hanun da aka yi rashin imani, ta kara da cewa ya zama dole soji su sa baki a al'amarin arewacin kasar.

Jami'in kungiyar, Mohamed Ould Abdine ya ce guntule hannu da aka yi a bisa tsarin shari'a ne : " Shari'a ta bukaci da a yi hakan."

Wani jami'in karamar hukumar ya ce mutane da dama ne suka ga lokacin da aka yanke hannun barawon. Ya kuma kara da cewa: "jini ya kwarara da dama yayinda aka guntule hannun wanda ya saci babur din acaban."

Ranar Lahadi, mutane da dama sun fito sun yi zanga-zanga a cikin garin Gao kusan kilomita dari daga Ansongo don hana 'yan kungiyar yanke hanun jama'a.

Mr Abdine ya ce ba wai sun fasa bane, kawai sun daga ranar gudanarwar ne.

Jami'ai daga kungiyar raya tattalin arziki na kasashen Afrika ECOWAS da kungiyar tarayar Afrika AU suna wani taro a Bamako, don tattaunawa akan sa bakin soji a alamuran Mali.

Kungiyoyin suna fatan samar da issasun bayanai game da kai jami'an soji ta yadda za su samu goyon bayan kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya wanda kawo yanzu bai amince da batun kai sojoji Mali ba, kamar yadda wakilin BBC na shiyar Afrika ta yamma, Thomas Fessy ya ce.

Karin bayani