Ana gab da karkare Wasannin Olympics

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasannin Olympics

Nan da sa'o'i kadan ne za'a fara fafatawa a rana ta sha biyar kuma ta jajiberin kammala gasar Olympics da ake yi a birnin London.

A bangaren guje-guje da tsalle-tsalle, za'a yi zagaye na karshe na tseren mita dubu biyar na maza, da kuma tseren mita dari takwas na mata, tare da tseren mika sanda na 'yan hurhudu na maza, inda cikin masu fafatawa har da mutumin da yafi kowa gudu a duniya, Usain Bolt.

A sauran wasanni kuma, masu gasar wasanni biyar na maza za su kara a fagen fadan takobi, da ninkaya, da kuma sukuwar dawaki.

Haka kuma Brazil za ta sami damar daukar lambar zinariya har guda biyu inda 'yan wasanta maza za su buga wasan karshe na gasar kwallon kafa tsakaninsu da kungiyar Mexico a filin Wembley, yayinda 'yan wasan Brazil mata za su yi arangama da kungiyar Amurka a wasan kwallon volley.

Karin bayani