Jama'a na barin Damaturu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani hari da aka taba kaiwa a Damaturu

Rahotanni daga jihar Yobe, arewacin Najeriya sun ce har yanzu jama'a na ci gaba da tururuwar ficewa daga Damaturu babban birnin jihar, saboda abinda suka ce, rashin tabbas din tsaron rayukansu da dukiyoyinsu.

A cikin 'yan makonnin da suka gabata dai al'amuran tsaro suka kara ta'azzara garin Damaturun, inda ake ta artabu tsakanin 'yan kungiyar da ake kira Boko Haram da jami'an tsaro a wasu unguwanni dake tsakiyar garin.

Tuni rundunar tsaro ta musamman dake jihar Yoben ta fitar da wata sanarwa dake cewa, jama'a su kwantar da hankalinsu su bar gudu suna barin garin.

A makon jiya ne dai gwamnatin jihar Yoben ta fitar da wata sanarwa tana yin kira ga mazauna birnin na Damaturu da su daina tururuwar kaura daga garin.