Mun mai da hankali ga wadanda suka tsira —Iran

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mutanen da girgizar kasar Iran ta raba da gidajensu

Hukumomi a Iran sun ce abin da suka mayar da hankali a kai bayan mummunar girgizar kasar ranar Asabar shi ne samar da abinci da matsuguni ga dubban mutanen da suka tsira da rayukansu.

Ministar lafiya ta kasar, Marzieh Vahid-Dastjerdi, ta ce ana kokarin tabbatar da cewa an kula da lafiyar wadanda abin ya shafa.

“Baya ga asibitocin wucin-gadi da aka kakkafa, shugaban Jami'ar Horar da Likitoci ta Tabriz ya amince ya samar da ayyukan kula da lafiya a duk wani tanti da ke kauyukan da al'amarin ya shafa”, inji ta.

A halin yanzu dai an dan sassauta da aikin ceto kasancewar an gano akasarin mutanen kauyukan da girgizar kasar ta daidaita.

Fiye da mutane dari uku ne dai suka rasa rayukansu yayin da fiye da dubu biyu suka jikkata.

Karin bayani