Ana taro a kan matsalar yunwa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani yaro da ke fama da yunwa a Afirka

A ranar Lahadi ne Firayim Ministan Birtaniya, David Cameron, zai karbi bakuncin taro a kan yaki da matsalar yunwa a duniya a matsayin daya daga cikin abubuwan da ba za a manta da su ba bayan gasar wasannin Olympics.

Mista Cameron ya ce a fili take cewa kasashen duniya sun gaza wajen shawo kan matsalar yunwar da ta gallabi kasashen Afirka.

Ya ce yara fiye da miliyan dari da saba'in ne ke fama da karancin abinci mai gina jiki.

'Yan siyasar kasashen Brazil, da Kenya da Bangladesh za su halarci taron, gami da wasu shahararrun 'yan wasa kamar dan kasar Habashan nan, Haile Gebreselassie.

Zakarun da suka yi nasara a gasar Olympics na bana sun ce za su marawa wannan yunkuri baya don shawo kan matsalar yunwa da yara kanana ke fama da ita a matalautan kasashen Afirka.

Karin bayani