An harbo jirgin saman Syria kusa da kan iyakarta da Iraki

syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jirgin saman da aka harbo kasa a Syria

Mayakan 'yan tawaye a Syria sunce sun harbo wani jirgin saman yakin gwamnati kusa da kan- iyakar kasar da Iraki.

An dai sanya hoton bidiyon harin a shafin Intanet.

Hotunan bidiyon na nuna yadda wani jirgi ya kama da wuta bayan karar harbin bindigar dake kakkabo jirgin.

'Yan tawayen dai, sunce sun kama matukin jirgin, amma kuma babu wata hanya da za a iya tabbatarda abinda suka ce.

Gidan talabijin din kasar Syrian dai, ya tabbatar da cewa wani jirgi yayi hatsari, amma ya ce sakamakon wasu matsaloli ne da jirgin ya fuskanta, kuma ya ce ana binciken inda matukin jirgin ya shiga.

Karin bayani