Ana ci gaba da neman jiragen saman Uganda da suka yi batan dabo

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Ugandan Helicopters

Ana can ana ci gaba da neman wasu jiragen sama masu saukar angulu guda biyu na sojin kasar Uganda da aka neme su sama ko kasa a kasar Kenya.

Jiragen suna cikin hudun da ya kamata su sauka a Kenya amma daya ne daga cikin su ne ya samu sauka a garin Garissa.

Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Kenya ya shaidan wa BBC cewa wani matukin jirgin ya tuntubi ma’aikatar daga tsaunin kasar Kenya.

Jirgin na daya daga cikin jiragen da aka tura Somalia don karfafa dakarun kungiyar tarayyar Afrika AU mai aikin samar da zaman lafiya a kasar wadda ake kira AMISON.

Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Kenya, Bogite Ongeri ya ce ba a da tabbacin ko matukin jirgin da ya tuntubi ma’aikatar tsaron ya yi hatsrine ko kuma ya ya sauka lafiya.

Ongeri ya kara da cewa Sojin kasar Kenya sun kaddamar da aikin neman jiragen ta kasa da kuma ta sama, amma rashin kyawun yanayi na janyo koma baya a aikin.

Ba a da tabbaci ko mutane nawa ke cikin jiragen.

Kakakin sojin Uganda Felix Kulayigye ya ce: “Har yanzu dai ana kan nema, saboda ba mu san abinda ya faru ba, amma yanzu haka ana ci gaba da bincike.”

Rundunar sojin Uganda na daga cikin dakarun AU da suke yakar kungiyar ‘yan gwagwarmaya ta Al-Shabab wadda ta yi wa kungiyar Al-Qaeda mubaya’a.

Duk da dai dakarun AU da wasu masu marawa gwamnatin Somalia da majalisar dinkin duniya ke goyon baya na cin galaba a kan ‘yan kungiyar Al-Shabab din, hakan bai hana su iko da kudancin da bangaren da ke tsakiyar kasar ba.

Rahotanni sun nuna cewa AU na shirye-shiryen kai wa kungiyar Al-Shabab hari a babban garin da suke rike da shi na Kismayo a cikin watan nan.

Al-Shabab sun kadammar da munanan hare-hare a Uganda wacce ita ce kasar da ta fi kowacce kasa a nahiyar Afrika bada gudunmawar dakaru na AU.

A shekarar 2010 ne mutane 76 suka rasa rayukan su a wani harin kunar bakin wake da kungiyar ta kai a wata mashaya da wajen cin abinci yayinda mutanen ke kallon gasar kwallon kafa ta duniya a Kampala.

Karin bayani