Wakiliyar Assad ta je China don tattaunawa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Buthaina Shaaban

Wata wakiliya ta musamman ga shugaba Basharul Assad na ganawa da ministan harkokin wajen China, Yang Jiechi, a yunkurin da gwamnatin Syria ke yi na kara samun goyon baya daga kasashen waje kan yadda take tunkarar rikicin kasar.

A baya dai China, tare da Rasha sun dakile yunkurin kasashen duniya na kakabawa kasar Syria takunkumi.

Tun da aka fara yaki a Syria Beijing ta kafe cewa ba za ta goyi bayan yunkurin kawar da shugaba Assad ba.

Don haka ziyarar da Buthaina ke yi a Beijing wani bangare ne a yunkurin da Assad ke yi wajen ganin kawayensa ba su juya masa baya a halin matsin da yake ciki ba.

Jami'an gwamnatin China sun ce watakila su gayyaci 'yan tawaye su ma domin tattauna a kan rikicin kasar.

Hakan na faruwa ne a lokacin da dakarun 'yan tawayen Syria suka ce sun harbo jirgin saman yaki mallakin gwamnatin kasar kusa da kan iyakarta da Iraq.

Wadansu hotunan bidiyo da aka sa a Intanet sun nuna jirgin ya kama da wuta yayin ake jin karar harbin bindigogi.

Gidan talabijin mallakin gwamnatin Syria ya tabbatar da faduwar jirgin, sai dai ya kara da cewa ya fadi ne sakamakon tangardar wata na'urarsa.

Idan dai ikirarin da 'yan tawayen suka yi na harbo jirgin saman yaki na gwamnatin ya tabbata, za a iya cewa hakan wata mahangurba ce ga shugaba Assad.

Karin bayani