BBC navigation

Dan kasuwan Burtaniya zai tallafawa matasan Najeriya

An sabunta: 14 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 17:03 GMT
droug richards

Droug Richards

Dan kasuwar nan na kasar Birtaniya, kuma tsohon tauraron shirin gidan Talabijin na Dragon's Den, Doug Ricahard ya kaddamar da wani shiri a Najeriya, da zai taimakawa matasa su bunkasa harkokin kasuwancin su.

Tsohon alkali a shirin gidan talabijin na Dragon's Den na fatan agazawa mutane kimanin 1,250 su fara harkokin kasuwancin a wani shiri karkashin tallafin Najeriya da gwamnatin Burtaniya.

Talauci da rashin aikin yi dai matsala ce da ta addabi kasashen yammacin Afirka da dama.

Mr Ricahard ya ce wannan mataki zai taimakawa matasa a Najeriyar bunkasa da karin kaifin basira a fannin kasuwanci, inda ya ce yana sa ran aiki da Najeriya, kasa mafi yawan al'umma a Afirka.

Yace: '' Ina fatan ganin cewa akasarin mutane 1,250 din da aka ware za a horar sun fara kasuwanci, kuma kasuwancin na bisa hanyar kaiwa ga nasara. Gwamnatin Najeriya ta ware kimanin dala miliyan 15 kwatankwacin fan miliyan tara da rabi don taimakawa fara kasuwancin.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.