BBC navigation

Tattalin arzikin Turai na ja da baya

An sabunta: 14 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 18:26 GMT

Kudin bai daya na Euro

Tattalin arzikin nahiyar turai yana ja- da baya.

Sabbin alkaluma sun nuna tattalin arzikin kasashe goma sha bakwai wadanda ke amfani da kudin euro yayi kasa da kashi daya cikin dari.

Wani wakilin BBC ya ce shugabannin kasashen Turai sun kasa cin nasara a kokarin da suke yi na magance koma bayan da ake fuskanta ta fuskar tattalin arziki, a yayinda ake cigaba da nuna damuwa game da rikicin basussuka.

Rashin bunkasar tattalin arzikin zai sa kasashe dake cikin matsala irinsu Spain su kasa tafiyar da harkokin kudaden su.

Wakilin na BBC ya kara da cewa kasashen Turai na fuskantar koma-bayan tattalin arziki, kuma irin tasirin da hakan ke yi, abu ne mai janyo fargaba ga tattalin arzikin Birtaniya, da kuma ga shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel dake ta fadi-tashi.

Shugaban kasar Faransa ya ce babu lokacin da ya dace a dauki matakan zaburar da tattalin arzikin da ya wuce wannan lokaci da muke ciki.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.