BBC navigation

Bam ya tashi a Kaduna

An sabunta: 14 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 19:21 GMT
Wasu jami'an tsaron Nijeriya

Wasu jami'an tsaron Nijeriya

Mutane kimanin ukku ne suka rasa rayikansu a garin Kaduna dake Arewacin Niajeriya, a sakamakon fashewar wani abu da ake kyautata zaton bom ne, a lokacin da wani ke dauke da shi a kan babur.

Ana kyautata zaton wanda ke dauke da bam din ya rasu tare da wasu karin mutane 2.

Lamarin dai ya auku ne a kan titin Ali Akilu, hanyar dake zuwa babban masallacin Juma'a na Sultan Bello.

Sai dai babu tabbas kan inda aka nufa da bom din.

A baya-bayan nan dai, garin na Kaduna ya fuskanci hare-haren bam wadanda suka hadassa asarar rayika da dama.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.