An hana musulmai yin sallar Idi a wani yanki na Jos

Image caption Jami'an tsaron Najeriya

Hukumomin tsaro a jihar Filato ta Nijeriya sun bukaci al'ummar musulmi da kada su je wani masallacin idi da ke wani yanki da mabiya addinin kirista suka fi rinjaye a birnin Jos yayin hidimomin karamar Sallah ta bana saboda dalilai na tsaro.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Abu Emmanuel, ya shaidawa BBC cewa an yanke wannan shawarar ce a lokacin wani taro da jami'an tsaro suka gudanar.

A cewarsa, ana takaddama a kan filin da musulmin ke yin Sallar Idi a ciki, kuma batun na gaban kotu don haka bai kamata a yi shisshigi game da batun ba.

Har yanzu dai kungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'a Wa'ikamatussunnah, wacce ta mallaki filin, ba ta mai da martani game da batun ba.

A bara dai an samu tashin hankali a birnin na Jos bayan da wasu mabiya addinin kirista suka yi wa musulmi kawanya yayin da suke Sallar Idi a masallacin da ke hanyar Rukuba.

Karin bayani