BBC navigation

Gwamnatin Syria na gabda rushewa -Hijab

An sabunta: 14 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 13:25 GMT
Tsohon Firai ministan Syria, Riad Hijab

Tsohon Firai ministan Syria, Riad Hijab

Tsohon Firai ministan Syria da ya sauya sheka, Riad Hijab ya ce kasar Syria na rugujewa ta fannin kimarta da kudadenta da kuma karfin sojinta.

Yayin da yake magana a Amman, babban birnin kasar Jordan, Mista Hijab ya ce gwamnatin Syria ba ta da iko da kashi talatin cikin dari na wasu yankunan kasar.

Ya kuma yi kira ga 'yan adawa dake kasashen waje su hada kansu, yayin da ya nemi sojojin Syria su koma bangaren mutanen kasar.

Shugabar hukumar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya Valerie Amos ta isa Syria domin duba hanyoyin da za a kara kai kayayyakin agaji cikin kasar.

Mista Hijab ya bayyana cewa ya koma bangaren 'yan adawa kuma ya bukaci 'yan siyasa da shugabannin soji su bar gwamnatin Assad.

Yace " Ina kira ga sojoji da su yi koyi da abin da ya faru a Masar da Tunisia, su koma bangaren mutanen kasa."

Wannan shi ne karo na farko da tsohon Firai ministan ya fito fili ya yi jawabi, tun bayan tserewar da yayi tare da iyalansa zuwa Jordan a makon jiya.

Kuma shi ne jami'I mafi girma da ya sauya sheka a gwamnatin Assad.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.