BBC navigation

Kamfanonin sayar da taba sun fuskanci koma-baya a Australia

An sabunta: 15 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 06:28 GMT

Kwalayen tabar da ke nuna illar shan ta

Gwamnatin Australia ta yi nasara a gaban babbar kotun kasar game da karar da ta shigar domin a tilastawa kamfanonin sayar da taba su rika sayar da ita a kwalaye marasa tambari.

A maimakon hakan, a cewar kotun, kamfanonin za su rika sayar da tabar ce a cikin korayen kwalaye, kuma dole kwalayen su kunshi hotunan mutanen da suka kamu da cututtukan da ke da alaka da shan sigari.

Farfesa Rob Moodie, masani ne a kan lafiyar jama'a a jami'ar Melbourne, kuma shi ne shugaban kwamatin kula da lafiyar jama'a da ya bayar da shawarar tilastawa kamfanonin sayar da taba bayyana irin illar da ke cikinta, ya ce hukuncin zai sauya dabi'ar mutane game da shan taba.

Ya ce:''Ina farin ciki matuka saboda a dalilin wannan hukunci mutane da yawa za su daina shan taba ballantana ta yi sanadiyar mutuwarsu.Bincikenmu ya nuna cewa idan ka ba matasa tabar da kwalinta babu wata alama, za ka ga idan tafiya tai tafiya, ba sa sha'awar shan tabar a cikin mutane.Hasalima hakan zai iya sanyawa su daina sha'awar shan tabar baki daya.

Babbar kotun da ke Sydney ta yi watsi da ikirarin kamfanonin sayar da tabar cewa cire tambarin zai yi kafar-ungulu ga kasuwancinsu.

Kasashen duniya da dama ne dai suka sanya ido a kan wannan sharia'a cikinsu har da Birtaniya, da Norway, da india, da ma Canada.

Su ma suna tunanin daukar irin wannan mataki, sai dai sun sanya ido ne don ganin ko kamfanonin sayar da tabar, wadanda ke da matukar tasiri a duniya, za su iya yin nasara a gaban kotu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.