BBC navigation

Birtaniya ta matsa lamba kan Ecuador

An sabunta: 16 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 06:52 GMT

Rafael Correa, Shugaban Ecuador

Gwamnatin Birtaniya ta kara matsa lamba kan Ecuador da ta bawa mutumin da ya kirkiro shafin Wikileaks mai kwarmata bayanai ta intanet Julian Assange, mafaka a ofishin jakadancin kasar da ke London a watan Yuni.

Ma'aikatar harkokin wajen Birtaniya ta ce ta na da ikon kwato Mr. Assange domin tasa keyarsa zuwa Sweden inda ake zarginsa da aikata laifukan da suka danganci jima'i.

Ministan tsaron Ecuador Ricardo Patino ya mai da martanin cewa kasarsa fa ba karkashin mulkin mallakar Burtaniya ta ke ba.

Yace idan kurarin da Birtaniya ta yi ya tabbata, za su dauki batun a matsayin takalar fada tare da keta alfarmar Ecuador, za kuma su mayar da kwakkwaran martani.

Mafaka

Lokacin da Julian Assange ya je ofishin jakadancin Ecuador ya nemi mafaka kusan watanni biyu da suka wuce; hukumomin Birtaniya sun ce ya ketare iyakar kamun yan sanda. Amma zai iya fuskantar kamen marsawar ya bar ofishin.

Yanzu da Hukumomin Birtaniya suka sanar da Ecuador cewa zata iya kama shi a karkashin dokar huldar diplomasiyya ta 1987. Ministan harkokin waje na kasar Ecuador Ricardo patino ya bayyana hakan a matsayin wata barazana ta zahiri wanda ya ce bai da ce ba ga kasar da ke bin turbar dimokradiyya wadda kuma take da wayewa.

Kakakin Maaikatar harkokin waje ta Birtaniya ya ce Birtaniya na fatan bangarorin biyu za su cimma daidaito ta diplomasiyya amma sun ce Birtaniyar na da hurumin tusa keyar Julian Assange zuwa kasar Sweden kuma tana da cikakken kudirin yin hakan, ko wane mataki kuwa Ecuadon ta dauka nan gaba a yau Alhamis.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.