BBC navigation

'Yan bindiga sun kai hari a Pakistan

An sabunta: 16 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 07:03 GMT

Hari a Pakistan

Sojin Pakistan sun ce wasu 'yan bindiga dauke da makamai masu sarrafa kan su da kuma gurneti sun kai hari kan daya daga cikin manyan sansanonin sojin sama da ke kusa da Islalmabad, babban birnin kasar.

Wani hafsan sojin sama yace 'yan bindiga sanye da kakin soji da kuma damarar bama-bamai sun shiga sansanin da ke Kamra, mai nisan kilomita sittin arewa maso yammacin Islamabad, bayan sallar Asubah.

Dakarun musamman na Pakistan sun kashe shida daga cikinsu yayinda soja guda ya rasu sannan wani babban kwamanda ya samu munanan raunuka a musayar wutar da aka yi.

Wakilin BBC yace wannan ne karo na uku da 'yan bindiga su ka iya keta tsaron wani muhimmin sansanin soji. Ko a bara ma 'yan bindiga sun kashe akalla jami'an tsaro goma a wani harin da suka kai sansanin sojin ruwa a garin Karachi da ke kudancin kasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.