BBC navigation

'Yan tawaye sun kashe sojoji 5 a Peru

An sabunta: 17 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 05:27 GMT

Sojoji a Peru

Dakarun soji a Peru sun ce 'yan tawaye sun hallaka sojoji biyar a dajin Junin da ke nisan kilomita dari uku daga Lima, babban birnin kasar.

Shugaban rundunar hadin gwiwa ta sojin kasar Admiral Jose Cueto yace a jiya, wasu dakarun su sun yi arangama da 'yan ta'adda.

Jami'in ya ce a artabun an kashe soji biyar, wasu biyar din kuma suka samu raunuka, yanzu haka su na asibitin soji da ke Lima yayinda aka mika gawarwakin mamatan ga iyalansu domin binnewa.

A shekarar alif dari tara da tamanin ne dai 'yan tawayen Shining Path masu ra'ayin gurguzu suka fara kai harin sari-ka-noke a kasar sai dai yanzu ana zarginsu da hada gwiwa da dillalan hodar iblis ta cocaine.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.