BBC navigation

Mutane na ci gaba da kauracewa kudancin India

An sabunta: 18 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 15:11 GMT
Dubban mutane na ci gaba da yin kaura daga kudancin India

Dubban mutane na ci gaba da yin kaura daga kudancin India

A kwana na hudu a jere dalibai da ’yan ci-rani wadanda suka fito daga jihohin arewa maso gabashin India suna ci gaba da barin wadansu biranen kudancin kasar, duk da kiran da hukumomi suka yi da su kwantar da hankulansu.

Dubban mutane ne dai suke barin wadansu manyan birane saboda jita-jitar da ake yadawa a shafukan sada zumunta na intanet wadanda ke cewa za a iya kai hari a kan wadanda suka fito daga yankin Assam da ma sauran jihohin arewa maso gabas saboda fadan kabilancin da ake yi a yankin Assam din.

Tuni dai wadansu jiragen kasa na musamman biyu dauke da dubban mutane suka isa Assam daga birnin Bangalore dake kudancin kasar.

Gwamnatin kasar ta India ta ce ta dauki dukkan matakan da suka dace don kare lafiyar al’umma, sannan kuma ranar Juma’a ta haramta aikewa da sakwanni da yawa ta wayar salula a yunkurinta na hana yaduwar jita-jitar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.