BBC navigation

Malema ya bukaci Shugaba Zuma ya yi murabus

An sabunta: 18 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 15:02 GMT
Shugaba Jacob Zuma ya ziyarci wadanda suka jikkata

Shugaba Jacob Zuma ya ziyarci wadanda suka jikkata sakamakon bude wutar da 'yan sanda suka yi

Dubban masu hakar ma'adinai na Afirka ta Kudu sun yi ta sowa da tafi yayin da tsohon jagoran matasa na jam'iyyar ANC mai mulki, Julius Malema, ke yi musu jawabi, inda ya yi Allah-wadai da 'yan sandan kasar.

A jawanin, wanda ya yi a wurin hakar ma’adinan da ’yan sanda suka harbe mutane talatin da hudu ranar Alhamis, tsohon jagoran matasan mai yawan jawo takaddama ya yi kira ga masu hakar madinan su dawo daga rakiyar Shugaba Jacob Zuma, sannan ya yi kira ga shugaban kasar da ya yi murabus.

Mista Malema ya kuma bukaci daukacin ma'aikatan ma'adinai a kasar su shiga yajin aiki, yana cewa, “Wajibi ne ma'aikata a sauran wuraren hakar ma'adinai su shiga yajin aiki don nuna goyon baya ga ma'aikatan da ke nan”.

Wannan jawabi na Mista Malema ya zo ne yayin da har yanzu—kwana biyu bayan hatsaniyar da ta kai ga harbe masu hakar ma'adinan a wata mahaka ma'adanin platinum—iyalan ma'aikatan da dama ba su san makomar danginsu ba.

Dangin ma'aikatan ba su makomarsu ba

Matan masu hakar ma'adinan sun koka da gazawar ’yan sanda da jami’an wurin hakar ma’adinan wajen samar da jerin sunaye guda daya na wadanda suka rasa rayukansu.

Baya ga wadanda suka rasa rayukan nasu dai mutane saba’in da takwas sun jikkata yayin da aka kama fiye da dari biyu.

Sai dai mai magana da yawun ’yan sandan, Kyaftin Dennis Adriao, ya shaida wa BBC cewa suna da niyyar tuntubar iyalan wadanda al’amarin ya shafa da zarar dama ta samu, amma hakan zai dauki lokaci.

“Zahiri muna bakin cikin abubuwan da suka faru ranar Alhamis har suka kai ga mutuwar mutane, kuma muna aiki kafada-da-kafada da jami'an ’yan sandan ciki da ma hukumar mahakar don tantance wadanda aka kashe da wadanda suka jikkata sannan kuma mu tuntubi iyalansu”, inji kakakin na ‘yan sanda.

Tun da farko dai Shugaba Jacob Zuma ya bayar da sanarwar cewa zai kafa wata hukumar bincike, yana mai bayyana mutuwar ma'aikatan da cewa abin bakin ciki ne.

Har yanzu ba a tabbatar da dalilan da suka sa ’yan sandan suka bude wuta ba, amma wadanda suka shaida faruwar al'amarin sun nuna cewa wani gungun masu zanga-zanga ne ya yo kan ’yan sandan.

Mista Zuma dai ya ce ya hakikance hukumar binciken za ta bankado gaskiyar abin da ya faru.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.