BBC navigation

Bama-bamai biyu sun tashi a Tripoli

An sabunta: 19 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 07:10 GMT
Tsohon shugaban Libya Gaddafi

Tsohon shugaban Libya Gaddafi

Jami'an tsaro a Libya sun ce wasu motoci makare da bama-bamai sun tarwatse a Tripoli, babban birnin kasar.

Ta farkon ta fashe ne kusa da ma'aikatar harkokin cikin gida ta biyun kuma daura da kwalejin 'yan sanda mata.

Fashewar ta ma'ikatar harkokin cikin gida ta hallaka mutane biyu tare da jikkata wasu da dama.

Wannan ne dai harin bom da ya yi kisa na farko a Libya tun bayan kifar da gwamnatin Muammar Ghaddafi a bara.

Shugaban tsaron birnin Tripoli Kanar Mahmoud Sherif ya ce magoya bayan Ghaddafi wadanda ya yi zargin su na samun tallafin daga abokan huldarsu a kasashe masu makwabtaka ne suka kai hare-haren.

A cikin watan nan ne dai gwamnatin rikon kwaryar Libya ta mika mulki ga zababbiyar majalisar dokokin kasar, a mika mulki cikin lumana na farko a tarihin kasar na baya-bayan nan.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.