BBC navigation

Shugaba Zuma ya ayyana makoki a Afirka ta Kudu

An sabunta: 19 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 20:11 GMT
Masu hakar ma'adinan da 'yan sanda suka kashe

Masu hakar ma'adinan da 'yan sanda suka kashe

Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu ya ayyana kwanakin makoki don nuna jimamin mutuwar mutane talatin da hudun da 'yan sanda suka harbe yayin wata zanga-zangar neman karin albashi.

Za a yi kasa-kasa da tutoci a ko ina a fadin kasar da ma ofisoshin jakadancinta da ke kasashen waje na tsawon wannan makon.

Shugaba Zuma ya kuma ayyana ranar Alhamis a matsayin ranar da hukuma ta ware don yin addu'o'i ga mamatan da kuma yunkurin samar da al'ummar da babu ruwanta da tashin hankali.

Ya kuma yi kira da a kafa wata hukumar bincike ta alkalai don ta binciki al'amarin.

Mista Zuma ya jaddada cewa har yanzu kasar na cikin dimuwa da radadi, sannan ya kara da cewa wajibi ne a samu lokaci a yi nazari a kan muhimmancin rayuwar bil-Adama.

Sannan ya bukaci kasar ta kauracewa nunawa juna yatsa.

Ministocin kasar da dama dai za su ziyarci garin da al'amarin ya faru don yin ta'aziyya.

An baiwa ma'aikatan wa'adin karshe

A halin da ake ciki kuma kamfanin da ya mallaki mahakar ma'adinan da al'amarin ya faru, Lonmin, ya baiwa ma'aikatan wa'adi na karshe su koma bakin aiki.

Wadansu daga cikinsu dai sun sha alwashin tsawaita kauracewa wuraren aikin nasu, suna cewa komawa cin mutunci ne ga abokan aikinsu talatin da hudu da ’yan sanda suka kashe.

Sun kuma ce za su koma wurin da suka yi zanga-zanagar su ci gaba da neman karin albashi.

Tun bayan fara yajin aikin fiye da mako guda da ya gabata, mutane arba'in da hudu sun rasa rayukansu yayin da saba'in da takwas suka jikkata.

An dai dora alhakin tashin hankalin ne a kan rashin jituwar da ke tsakanin kungiyoyin kwadago yayin yajin aikin na neman karin albashi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.