BBC navigation

An samu ci gaban siyasa a Somalia

An sabunta: 20 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 20:06 GMT
Sabbin 'yan majalisar dokokin Somalia

Sabbin 'yan majalisar dokokin Somalia

Somalia ta sami sabuwar majalisar dokoki, kuma su ne na farko tun lokacin da aka hanbarar da gwamnatin Kasar a shekarar 1991.

An rantsar da mambobin majalisar su 211 wadanda dattijan Kasar suka zaba a birnin Mogadishu, daya daga cikin birane dake da cikakken tsaro.

Kamar yadda al'ada ta nuna, kakakin majalisar dokokin Kasar mai rikon kwarya shine dan majalisa mafi jimawa wato Janar Muse Hassan.

Kuma shine zai jagoranci Kasar har zuwa lokacin da 'yan majalisar zasu zabi sabon shugabanKasa.


A yau ne ya kamata a ce an kawo karshen mulkin gwamnatin rikon kwaryar kasar ta Somalia, da zaben shugban kasa.

Sai dai kuma hakan bai yiwu ba ya yin da da kyar aka samu tantance 'yan majalisar.

Inda aka dauki akalla kwanaki 10 kafin a samu yawan 'yan kwamitin da za su tantance wadanda za'a zaba a matsayin 'yan majalisar.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.