BBC navigation

Shugaba Assad zai iya sauka ba tare da sharadi ba

An sabunta: 21 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 18:58 GMT
Mataimakin praministan Syria

Mataimakin praministan Syria

Mataimakin PMn Syria yace a shirye gwamnatin Kasar take ta gudanar da tattaunawar saukar Shugaba Bashar Al Asad daga kan mulki, a wani bangare na tattaunawar da za'a gudanar ba tare da sanya wasu sharudda ba, wacce za kuma ayi ta da nufin kawo karshen wata da watannin da aka shafe ana rikici a Kasar.


Qadri Jamil ya yi wadannan kalamai ne a wani taron manema labaru a Moscow.


Amma yace ba zasu amince da duk wata bukata ta tunbuke Shugaba Asad a matsayin wani sharaddi ba kafin a soma tattaunawar .


Mr Jamil wanda aka nada shi a cikin watan Yuni ya taba fadi a a baya cewar, ba za iya warware matsalolin Syria ta hanyar daukar matakin soji ba.

A wani fadan baya bayan nan da ake a Syria, masu fafutuka 'yan adawa da kuma magidanta sunce an kashe akalla matasa ashirin, an kuma harbi da dama daga cikin su, a lokacin da dakarun gwamnatin Syrian suka kwace wani yanki dake wajen birnin Damscus.


Dakaru da kuma tankunan yaki na ta shawagi a Mouadamiya bayan an shafe kwanaki biyu ana luguden wuta.


A birni na biyu mafi girma a Syrian wato Aleppo, 'yan adawa sunce hare haren da jiragen yakin gwamnatin kasar suka kaddamar yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.