BBC navigation

Juncker na adawa da fitar Girka daga cikin kasashen kudin Euro

An sabunta: 22 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 20:10 GMT
Juncker da Samaras

Juncker da Samaras a tattaunawar da suka yi

Shugaban kungiyar ministocin kudi na kasashen da ke amfani da kudin Euro, Jean Claude Juncker, ya ce baya goyon bayan kasar Girka ta daina amfani da kudin bai daya na Euro.

Ya bayyana haka ne a birnin Athens lokacin da yake ganawa da Pirayim Ministan Girka, Antonis Samaras.

Mista Juncker ya ce abu mafi mahimmanci shi ne kasar ta fito da wani tsari na rage gibin basukan da ake binta, ta yadda za a ba ta karin wani bashin na ceto tattalin arzikinta.

Tun da farko dai, Mista Samaras ya ce Girka ta shirya rage kasafin kudinta da kusan Euro biliyon 11 da rabi don farfado da tattalin arzikinta.

Mista Samaras ya ce, suna aiki don samun daidaito da kuma tabbatar da cewar sun cimma burin ficewa daga cikin wannan matsalar.Wannan tattaunawa dai daya ce daga cikin muhimman tattaunawa uku da Mista Samaras zai yi a cikin wannan makon.

Zai tattauna da shugabannin Faransa da Jamus

Zai tattauna da Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel a birnin Berlin ranar Juma'a, daga bisani kuma zai gana da Shugaban Faransa Francois Hollande ranar Asabar.

Tattaunawar za ta mayar da hankali ne a kan shirye-shiryen Girka na zabtare kudaden da ta ke kashewa da euro miliyan goma sha daya da dubu dari biyar, tana fatan hakan zai sa ta samu kudaden da za su ceto tattalin arzikin ta nan gaba.

Mista Samaras ya ce zai tabbatar wa kasashen da ke amfani da kudin euro alkawarin da Girka ta yi tare da fito da wadansu sababbin hanyoyi don farfado da arzkin kasar

Ya kara da cewa Girka ta fuskanci matsala saboda zaben da aka gudanar a bana, don haka sai a hankali kasar da mutanenta za su farfado daga radadin da suka shiga.

A farkon wannan makon dai shugabannin kasashen Turai sun tabbatar da cewa sun duba yiwuwar ficewar Girka daga sahun kasashe masu amfani da kudin euro.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.