BBC navigation

An binne mutanen da aka yiwa kisan kiyashi a Kenya

An sabunta: 23 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 17:51 GMT
Taswirar Kenya

Taswirar Kenya

A kudu maso gabashin Kenya, an binne mutane hamsin da biyar din da suka rasa rayukansu a wani kisan kiyashi a kabari guda.

Mutanen, wadanda galibinsu mata ne da kananan yara, sun rasa rayukansu ne a wani tashin hankali mai nasaba da kabilanci.

An dai bayyana kisan kiyashin da cewa kazantacce ne wanda rabon da a ga irinsa tun shekarar 2001.

Mahara dauke da adduna da bindigogi ne dai suka far wa kauyen Raketa da ke gundumar Kogin Tana da sanyin safiya.

Wani magidanci ya bayyana cewa maharan sun zagaye kauyen, sannan suka sanyawa gidaje wuta.

Gidaje kusan dari da ashirin aka kona.

Fito-na-fito tsakanin kabilu

A dan tsakanin nan manyan kabilun yankin su biyu—Pokomo da Orma—sun sha yin fito-na-fito sakamakon takaddamar da suke yi a kan filaye.

’Yan kabilar Pokomo sun ce makiyaya na kabilar Orma sun kada shanu cikin gonakinsu.

Ana yawan samun rikice tsakanin kabilun kasar Kenya musamman ma a lokacin rani a kan filaye da kuma albarkatun.

Masu fafutukar kare muhalli sun ce dumamar yanayi ce ke kara assasa rikicin.

Rahotanni sun bayyana cewa wani rikicin ya barke a Mandera, a arewa maso gabashin kasar, inda mutane tara suka rasa rayukansu ranar Litinin.

Duk da kasancewar ’yan sanda masu dimbin yawa a yankin, ana ci gaba da zaman dardar saboda fargabar yiwuwar kai hare-haren daukar fansa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.