BBC navigation

An kashe akalla mutane 50 a Kenya

An sabunta: 22 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 15:44 GMT
Rikici a Kasar Kenya

Ana cigaba da rikicin kabilanci a kudu maso gabacin Kenya

'Yan sanda a Kenya sun ce an kashe akalla mutane 50 a wani tashi hankali mai nasaba da kabilanci da aka yi a Kudu maso Gabashin kasar.

Galibin wadanda aka kashe, mata ne da kuma kananan yara.

Rahotanni sun ce fadan tsakanin wasu kabilun biyu da ba sa ga maciji da juna a lardin Kogin Tana, ya samo asali ne daga wata jayaya kan batun mallakar filaye da burtali.

Wannan dai shi ne tashin hankalin kabilanci mafi muni da aka yi a kasar ta Kenya, tun bayan zaben kasar da aka yi a shekara ta 2007.

Hakazalika, an bada rahoton kisan wasu karin mutanen fiye da 10 tun ranar Litinin a Arewa maso Gabashin kasar.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.