BBC navigation

Gawar Meles Zanawi ta isa gida Ethiopia

An sabunta: 22 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 06:40 GMT

Marigayi Meles Zanawi tsohon Fara ministan Ethiopia

An kai gawar Fara Ministan Ethiopia birnin Addis Ababa daga birnin Brussels wurinda ya rasu bayan wata doguwar rashin lafiya ranar litinin.

Daruruwan dubban mutane ne dake dauke da kyandira suka rika bin motarda ta dauko gawar a yayinda da ake ratsawa da ita a cikin birnin.

A can birnin Brussels inda ya rasu dai wani sahun masu daukar gawa tare da rakkiyar 'yan sanda mahaya babura ne suka fitarda gawar tasa daga wani hotel dake daf da asibitin da ya kwanta zuwa wani karamin filin tashin jirage na soji.

Sojoji da 'yan sandan Belgium sun tsaya har sai da suka ga an shigar da akwatin gawar cikin wani jirgin kanfanin zirga-zirgar jiragen sama na Ethiopia.

Isa gida

Sa'oi bayan haka aka fitar da akwatin daga cikin jirgin a birnin Adis Ababa lullube da tutar kasar mai launukan kore da ruwan-zinari da kuma ja.

A wajen da jirgin ya tsaya kanuwarsa ta zubar da hawaye tana cewar ''yayana ya kaunaci kasarnan ya cancanci fiye da hakan''.

A can wajen filin jirgin dubban masoyansa sun yi dafifi a cikin ruwan sama domin yin tarbon gawar tasa.

Wasu na dauke da alluna da aka rubutawa sakonnin ''Meles ayyukanda ka yi ba zasu mutu ba.''

Titin da ya tashi daga filin jirgin saman ya cike take taf da mutane da kuma motoci har zuwa gidansa inda aka ajiye gawar tasa domin mutane su yi masa kallon bankwana da karramawa.

Wasu masoyansa dai sun yi ta kukan mutuwar wanda suka ce ya ceci kasar da ta dade cikin wahala.

An dai riga an yi sanarwar cewar kasar ta shiga kwanakin zaman makoki kuma shirye-shiryen jana'izar sa sun kankama.

Ra'ayoyi kan mutuwarsa

Amurka dai ta yaba shi a zaman babban abokin kawance saboda yakin da ya daura da masu tsattsauran ra'ayi duk da cewar juriyar sa ga masu adawa dashi 'yar takaitacciya ce ainun.

Sai dai masu adawa dashi sun yi marhabin da mutuwar wanda suka kira'' mai mulkin malaka'u'' inda har wata kungiyar ta kira shi '' mugun sarki mai kisan kiyashi''.

A daidai lokacinda gawar tasa ta isa gida Ethiopia daga kasar Belgium inda ya rasu da daren jiya, kasar ta shiga cikin wani babban rashin tabbas kan makomar siyasar ta inda wasu ke ganin yanzu zata samu shugabanci mai rauni.

Meles ya kwashe shekaru 21 ne yana shugabancin kasar dake kusurwar Afrika.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.