BBC navigation

Zaben Amurka: Dan takarar senata yayi katobara

An sabunta: 22 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 08:27 GMT

Senata Todd Akin dan takarar dan majalisar dattawan Amurka

Dan takarar Shugaban kasa na jam'iyyar Republican a Amurka Mitt Romney ya yi kira ga wani dan takarar jam'iyyar da ya kawo karshen yakin neman zaben da yake yi a majalisar dattawa bayan ya yi wasu kalamai dake tattare da rudani dangane da fyade.

Todd Akin wani dan majalisa ya sa zaure majalisar ya rude bayan ya yi batun cewar jikin mace zai iya kare ta daga daukar ciki a wasu lokuttanda ake yi mata fyade.

Mr. Akin wanda ke kokarin nuna adawarsa ga zubar da ciki daga bisani ya nemi afuwa.

Sai dai kuma ya ki janyewa daga takarar da yake yi ta dan majalisar dattawa daga jihar Missouri.

'' Ra'ayinsa ne ''

Mr. Mitt Romney ya ce ba zai iya kaare Mr Akin ba ga wannan maganar da yayi.

"kalaman da ya yi a kan batun fyade matukar cin fuska ne, kuma ba zan kare abinda ya fada ba, ba zan kare shi ba." inji Romney.

'yan jam'iyyar Republican suna kallon jihar ta Missouri a matsayin wani wurin da za a fafata a lokacin zabe a kokarin da suke yi na doke karamin rinjayen da 'yan jam'iyyar Democrat ke da shi a majalisar dattawan kasar.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.