BBC navigation

Jihohin Nijeriya za su karbi bashin $500m

An sabunta: 23 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 20:32 GMT
shugaba Goodluck Jonathan na Nijeriya

shugaba Goodluck Jonathan na Nijeriya

A Najeriya, Majalisar tattalin arzikin kasar ta amince wa wasu jihohi su karbo rancen dala miliyan dari biyar don inganta rayuwar al'ummominsu.

Za a yi amfani da kudaden ne dai wajen yaki da kwararar hamada da zaizayar kasa da kuma matsalar ambaliyar ruwa.

Wannan amincewar ta zo ne a daidai lokacin da wasu 'yan Najeriyar ke kukan cewa kasar ta kama hanyar fadawa cikin kangin bashi.

Majalisar tattalin arzikin Najeriyar ta bayyana cewa 'yan kasar da dama na fama da matsaloli daban-daban da suka hada da talauci da rashin aikin yi, saboda haka akwai bukatar farfado da tattalin arzikin kasar ta yadda rayuwar jama'a za ta inganta.

Kuma wannan ne ya sa majalisar ta amince wa wasu jihohin kasar karbar rancen daga wasu bankunan kasa da kasa ciki har da bankin musulunci, da Bankin Bunkasa nahiyar Afirka.

Sai dai wannan yunkuri na sake karbo bashi da gwamnatin Najeriyar ta ba da kafa na janyo ma ta suka daga 'yan kasar da dama, ciki har da babbar jam'iyyar adawar kasar A C N, wadda ke cewa ba daidai ba ne a sake jefa kasar cikin kangin bashi, kasa da shekara bakwai da Paris Klub ta yi wa Najeriya ahuwar bashin da ya kai dala miliyon dubu talatin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.