BBC navigation

An wallafa hotunan Yarima Harry na Burtaniya tsirara

An sabunta: 24 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 09:04 GMT
Yarima Harry

Yarima Harry

Jaridar the Sun ta Birtaniya, ta zamanto ta farko da ta wallafa hotunan Yarima Harry mai jiran gadon sarautar Ingila na uku, tsirara tare da wata mata a wani otel a birnin Las Vegas na Amurka.

Hotunan biyu dai sun bayyana ne lokacin wata shakatawar sirri ta karshen mako da Yariman ya yi da abokansa, kuma an bayyana cewa hotunan da suka nuna Yariman tare da wata mata tsirara a wani dakin otal, an dauke su ne da abin daukar hoto na wayar salula a ranar Juma'ar da ta gabata.

Jaridar ta ce, ta yi amannar cewa, masu karanta ta, na da hurumin ganin hotunan da tuni aka wallafa su a sassan duniya da dama.

Ta ce, yadda kafafen watsa labarun Birnitaniya suka bayar da labarin, ya haddasa zazzafar muhawara tsakanin alummar kasar.

Kamfanin da ya mallaki jaridar mai suna News International, ya ce kamfanin ne ya yi wannan yunkuri duk kuwa da gargadin da lauyoyin iyalan masarautar Burtaniyan suka yi na cewar ya zama wani katsalandan cikin harkokin da suka shafi sirrin Yariman.

Dalilin Buga wa

Hotunan dai sun fara bayyana ne a wani shafin internet na Amurka TMZ a cikin makon baya bayan nan.

A shafin jaridar The Sun din ta ranar Juma'a, an rubuta babban take ''Hoton Harry a tsirara, kun riga kun gani a shafukan internet''.

Babban Editan jaridar the Sun David Dinsmore ya ce, jaridar ta yi zurfin tunani game da wallafa wadannan hotuna, ya kara da cewa: '' A gare mu wani abu ne na 'yancin 'yan jarida.

"Wannan wani yanayi ne na yadda miliyoyin jama'a zasu iya ganin hotuna a fadin duniya a shafukan intanet, wanda kuma ba zaka taba gani a shafukan jaridu masu tagomashi na kasar ba da miliyoyin jama'a ke karantawa.

"Wannan wani abu ne game da yadda masu karanta shafukan jaridunmu za su samu abin tattaunawa da mutumin da shine na uku a kan layin jiran gadon sarauta, abu mafi sauki kenan."

Shawarar Editoci

"Wannan wani abu ne game da yadda masu karanta shafukan jaridunmu za su samu abin tattaunawa da mutumin da shine na uku a kan layin jiran gadon sarauta, abu mafi sauki kenan."

David Dinsmore, Editan jaridar The Sun

Fadar Sarauniyar Ingila ta St James ta tuntubi Hukumar Karbar koke-koken game da Kafafan Yada Labarai (PCC) ranar Laraba saboda ta ce ta damu matuka game da shiga sirrin Yarima mai shekara 27, tare da keta dokar aikin editoci ta kasa.

Fadar ta ce ta ji cewa akasarin jaridun kasar Burtaniya na tunanin amfani da hotunan, duk da cewa babu ko da guda yanzu.

A martani ga matakin da jaridar the Sun ta dauka, mai magana da yawun fadar ta St James, ya ce: ''Mun bayyana matsayinmu game da sirrin Yarima Harry, saboda haka wallafa hotunan wata shawara ce da Editocin suka dauka.

'' Bamu da sauran ta cewa walau kan wallafa hotunan, ko kuma shi kan sa gundarin labarin da ya shafi hutun cin gashin kansa da Yarima Harry ya yi a Las Vegas.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.