BBC navigation

Wani malami ya mutu a rikicin addini a Lebanon

An sabunta: 24 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 19:17 GMT
mayaka

wasu mayakan 'yantar da Syria

An kashe mutane uku, ciki har da Sheikh Khaled al-Baradei, wani malamin Sunni a Tripoli, birnin na biyu mafi girma a Lebanon, yayinda rikicin addini ke kara kamari, wanda kuma tashin hankalin da ake yi a Syria ya kara iza wutarsa.

Mutanen sun mutu ne a lokacin rikici tsakanin 'yan Alawite 'yan tsiraru, da 'yan Sunni, wadanda ke da rinjaye a birnin na Tripoli.

Mutane akalla goma sha biyar aka kashe a tashin hankalin da aka yi cikin wannan makon.

Fadan dai na daukar irin salon wanda ke faruwa ne a Syria, inda shugaban kasar, Bashar al-Assad, mai bin akidar Alawite, ke ta kokarin murkushe boren da galibi 'yan Sunni ke yi ma gwamnatinsa.

Dakarun sojan Lebanon sun shiga anguwannin da tankokin yaki, amma ya zuwa yanzu sun gaza dawo da bin doka.

Praministan Lebanon, Najib Mikati, yayi kira ga dukkan bangarorin da su bada hadin kai ga matakan da rundunar sojan kasar take dauka na kawo karshen rikicin.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.