BBC navigation

An yankewa Anders Breivik hukuncin dauri

An sabunta: 24 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 16:10 GMT
Anders Behring Breivik

Anders Behring Breivik

Wata kotu a Norway ta yanke hukuncin cewa mutumin nan da ya kashe mutane saba'in da bakwai a watan Yulin bara, Anders Behring Breivik, na da cikakken hankalinsa, don haka ta daure shi na tsawon shekaru ashirin da daya a gidan kaso bisa laifin aikata kashe kashen.

Su dai masu gabatar da kara sun nemi a bayyana cewa yana da tabin hankali ne, domin a kai shi a garkame a wani wuri mai tsauraran matakan tsaro da ake tsare masu tabin hankali.

Alkalin da ta yanke hukuncin, Mai Shari'a Wenche Elizabeth, ta bayyana hukuncin na daurin shekaru ashirin da daya da shekaru goma mafi karanci a bisa tanade-tanaden wadansu sassa na dokokin Penal Code.

Breivik dai ya yi ta nanata cewa ya kashe mutane saba'in a hare-haren bom da na bindiga da ya kai amma bai nuna wata alama ta yin nadama ba.

Daukaka kara

A baya dai ya taba fadin cewa ba zai daukaka kara a kan hukuncin da za a yanke masa ba.

Mai Shari'a Wench Elizabeth ta karanta hukuncin ne a gaban akasarin mutanen da suka tsira da rayukansu lokacin da Breiviki ya kai hare haren da iyalan wadanda suka mutu.

Daya daga cikin wadanda suka tsira da rayukan nasu, Tore Sinding Bekkedal, ya ce ya yi alfahari da hanyar da aka bi wajen yanke hukuncin.

“An bi hanyar da ta kamata wajen yanke wannan hukunci a wannan shari'a mai 'yanci da kotu mai 'yanci ta yanke”, inji Bekkedal.

A baya dai Breivik ya ce ya yi nufin kai harin ne a kan jam’iyyar masu matsakaicin ra'ayi ta Labour dake mulki a kasar saboda goyon bayan da take baiwa Musulmi 'yan cirani.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.