BBC navigation

'Yan kasar Syria 200,000 sun yi gudun hijira

An sabunta: 24 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 16:07 GMT
sansanin 'yan gudun hijira

'yan gudun hijira na karuwa a makotan syria

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce 'yan gudun hijirar Syria dubu 200 sun tafi kasashe makwafta yayin da rikicin kasar ya yi kamari.

Hukumar ta ce tuni wannan adadi ya kai fiye da jumlar da ta yi hasashe zuwa karshen shekarar da ake ciki.

Ta ce wasu 'yan gudun hijira dubu 30 sun tsallaka zuwa Turkiya a cikin mako guda kawai.

Wani kakakin hukumar kula da 'yan gudun hijirar ta Majalisar Dinkin Duniya ya kara da cewar yanayin tsaron da ke tabarbarewa a Lebanon ya kawo cikas ga aikinta na taimakawa 'yan gudun hijira a can.

Rahotanni sun bayyana cewa luguden wutar da sojan Syria ke yi wani bangare ne na kokarin da gwamnati ke yi na karbe iko da garuruwan da ke wajen garin.

Rikicin Syria

Rikicin na Syria ya yi matukar yin tasiri, ga rayuwar 'yan kasar, wanda fiye da mutane dubu dari biyu ne su ka yi rijista da hukumar ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya a makwaftan kasar tun bayan da dakarun tsaron kasar suka fara murkushe masu rajin kare mulkin dumokradiya.

Mai magana da yawun hukumar, Adrian Edwards, ya shaidawa manema labarai a wani taro da aka gudanar a Geneva cewar, ''a yanzu mun samu yawan 'yan gudun hijirar da suka kai 202, zuwa ,512 a wajenmu''

Ya kara da cewa, ''mun samu rahoton 'yan gudun hijira 2,200 da suka tsallaka iyakar Jordan da daddare, kuma an karbe su a sansanin Za'atari da ke arewacin kasar''.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.