BBC navigation

Samsung zai biya Apple tarar dala biliyan daya

An sabunta: 25 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 07:24 GMT
Wayoyin Salula

Wayoyin Salula Samfurin Samsung da Apple


Masu taimakawa alkali yanke hukunci a Amurka, sun yanke hukuncin cewa katafaren kamfanin fasahar nan na kasar Korea ta Kudu wato Samsung ya saci wasu fasahohi daga kamfanin Amurka na Apple wurin kera ta sa wayoyin na hannu.

An shafe shekara guda dai ana kai komo na shariah, wanda ya kunshi zarge zarge kimanin dari bakwai.

Bayan shekara guda da shigar da kara wanda ta binciki ikirarin karya doka, wata kotu a birnin California ta bayar da umarnin cewa kamfanin na Samsung ya biya tarar sama da dala biliyan daya na dameji.

Alkalan dai sun yi watsi da musanta ikirarin na su da kamfanin na Samsung yayi, da mai yiwuwa ya ce zai daukaka kara game da yanke shawarar da suka yi.

Shekara guda ke nan da sa in sa marar dadi dake wanzuwa tsakanin manyan kamfanonin fasahar kera wayoyin salula da na'urori masu kwakwalwar da suka mamaye kasuwannin duniya.

Kamfanin Apple dai ya zargi kamfanin na Samsung da yin satar dabarun fasahar kere-kere wajen kera nasa samfurin wayoyin salular ne da kananan na'urori masu kwakwalwa, sai dai Kamfanin Samsung ya sake shigar da wata karar musanta cewa ya aikata hakan, inda ya ce ya samu dabarun fasahar ne daga wasu kamfanonin.

Bayan kwanaki biyun da aka shafe ana muhawara game da batun, masu taimakawa alkalin sun yanke hukuncin cewa kamfanin Samsung na kasar Korea ta Kudun ya aikata satar dabarun fasahar kere- kere har samfurin zayyene-zayyane biyar zuwa shida, inda suka bukaci ya biya tarar sama da dala biliyan daya.'

Manyan kamfanonin kera wayoyin salular da na'urori masu kwakwalwar dai sun jima suna sa in sa da zargin junansu a kasashe da dama.A jiya ne dai wata kotu a Korea ta Kudu ta yanke hukuncin cewa duka kamfanonin biyu keta doka wajen satar fasahar kere-keren junansu.

Takunkumi ga Kamfanin Samsung

Mai yiwuwa Kamfanin na Apple zai bukaci hana shiga da wasu daga cikin kayayyakin da kamfanin na Samsung ke kerawa cikin kasuwannin Amurka, sai dai kamfanin na Samsung ya ce zai daukaka kara game da yanke hukuncin.

"zamu yunkura da gaggawa mu shigar da kara domin dakushe wannan hukunci a wannan kotu, amma idan bamu yi nasara ba, zamu kara gaba zuwa Kotunan Daukaka kara,'' kamar yadda wasu bayanai suka fito daga kamfanin na Samsung.

Kamfanin Samsung din dai ya bayyana sakamakon hukuncin a matsayin '' asara ga masu sayen kayyakinsu a Amurka''.

"zai haifar da karancin zabi, da kuma karancin samun sabon abu, kana kuma sayen kayayyakin da tsada,'' in ji kamfanin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.