BBC navigation

Kisan malami: Ana tarzoma a Mombasa

An sabunta: 27 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 14:56 GMT

Aboud Rogo Mohammed

Tarzoma ta barke a birnin Mombasa da ke gabar tekun Kenya bayan an bindige wani malamin addinin Musulunci da ake zargin yana goyon bayan masu tsattsauran ra'ayi na Somalia.

'Yan sanda sun ce malamin, Aboud Rogo Mohammed, da mai dakinsa suna cikin tafiya a motarsu wadansu 'yan bindiga suka bude musu wuta.

'Yan sandan sun kuma musanta rahotannin da aka bayar tun da farko cewa su ne suka bindige malamin.

An kashe mutum guda an kuma jikkata da dama a hatsaniyar da ta biyo baya.

Mista Rogo na cikin jerin mutanen da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa takunkumi saboda zargin cewa yana tallafawa mayakan al-Sahabaab da kudi.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.