BBC navigation

An saurari bahasi a shari'ar yiwa yaro fyade

An sabunta: 27 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 16:07 GMT
Taswirar Najeriya

Taswirar Najeriya

Wata babbar kotun Musulunci da ke Gusau, babban birnin Jihar Zamfara a arewacin Najeriya, ta fara sauraron bahasi daga shaidu a kan zargin da ake yiwa wadansu ’yan mata uku na cin zarafi wani saurayi har ya suma.

Da farko dai rahotanni sun ce matan ’yan tsakanin shekaru ashirin zuwa ashirin da uku sun tilastawa saurayin yin jima’i da su ne daya bayan daya har ya suma.

Sai dai duka bangarorin—masu shigar da kara da wadanda ake karar—sun ce ba haka batun yake ba.

Mai shigar da karar, Hamisu Ibrahim Gusau, ya bayyana cewa, “Muna zarginsu da ainihin hada baki da kuma cin zarafi a kan musgunawa wannan yaro da suka yi.

“Shi matsayin jami’in tsaro ne wurin sun yi wa [’yan matan] horo su bar surutu, su bar amfani da waya suna kade-kade suka ki bari, shi ne suka fid da [’yan matan] waje. To a sanadiyyar haka ne, sai ’yan matan suka rufarwa wannan yaro wanda ake kira Abdurrahman Sulaiman, suka yayyaga mishi kaya, suka fid da al’aurarshi waje suna ta ja har sai da ya suma a wurin”.

Su ma ’yan matan dai sun ce kazafi aka yi musu, kamar yadda babbar cikinsu, Rahanatu Ibrahim mai shekaru ashirin da uku, ta shaidawa BBC.

“An cuce mu an ji mana ciwo, sannan an zo an nuna mana mulki da kudi; an mana kazafi an yada mu a duniya—kazafin cewa wai mun yiwa yaro fyade. To duk duniya kowa ya ce bait aba jin inda mace ta yiwa namiji fyade ba”.

Lauyan da ke kare ’yan matan ya ce suna shirin daukar mataki na shari’a a kan kafofin yada labaran da suka yada cewa sun yiwa yaro fyade.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.