BBC navigation

Ana samun karuwar Fashin jiragen ruwa a tekun yankin Afirka ta yamma

An sabunta: 28 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 17:35 GMT
Fashin teku

Fashin jiragen ruwa a tekun yankin Afirka ta yamma ya karu

Wasu 'yan fashin kan teku sun yi garkuwa da wani jirgin ruwan dakon mai na kasar Girka a kan tekun dake kusa da kasar Togo

'Yan fashin sun yi awon gaba da ma'aikatan jirgin ruwan su sama da shirin, bayan musayar wuta.

Hukumar kula da sufurin jiragen ruwa ta duniya ta ce an samu karuwar fashin jiragen ruwa a tekun dake yankin Afrika ta Yamma, inda aka yi fashin jiragen ruwa shidda, ya zuwa yanzu a bana.

Hukumar tana rike da jiragen ruwan, har zuwa tsawon lokacin da za a kwashe ana kwashe kayan dake cikinsu zuwa cikin wasu jiragen ruwan.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.