BBC navigation

Mutuwar mai fafutuka tsautsayi ce —Kotun Isra'ila

An sabunta: 28 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 16:25 GMT
Rachel Corrie

Rachel Corrie

Wata kotu a Isra'ila ta yanke hukuncin cewa mutuwar wata ba-Amerikiya mai fafutuka, wacce katafila ta bi ta kanta shekaru tara da suka wuce a Gaza, tsautsayi ce.

Rachel Corrie, wacce ke sanye da riga mai ruwan goro, ta rasa ranta ne yayin da take kokarin hana katafilar rushe wadansu gidajen Falasdinawa a Rafah.

Kotun ta bayyana cewa mutuwar matashiyar abin damuwa ne, amma ta danganta mutuwar da cewa gini ne ya fado mata.

Lauyan da ke wakiltar gwamnatin Isra’ila, Irit Kiman, ya ce ba za a iya sukar halayyar sojojin da suke da hannu a wannan al'amarin ba.

“Kotu ta saurari duk jawaban jami'ai da sojojin da suke wajen da al’amarin ya faru, kuma ta gamsu da dukkan bangarorin, don haka ya zama dole a yi watsi da karar”, inji shi.

'An keta dokar kasa-da-kasa'

Lauyan da ke tsayawa iyalan Rachel, Hussein Abu-Hussein, ya ce Isra’ila ta karya dokar kasa-da-kasa a wannan shari'a.

“Wannan hukunci ya gurbata hujjoji kwarara da aka gabatar a kotu, sannan ya saba da dokokin kasa-da-kasa dangane da batun masu kare hakkin bil-Adama.

“Wannan hukunci ya fito karara ya nuna yadda aka kasa gurfanar da sojojin Isra’ila don su amsa tuhumar ci gaba da cin zarafin bil-Adama”.

Bayan yanke hukuncin, mahaifiyar Rachel, Cindy Corrie, ta ce rana ce mai matukar muni ga harkar kare hakkin bil-Adama, da tsarin shari’a da ma Isra’ila.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.