BBC navigation

Mitt Romney ne dan takarar Republican a Amurka

An sabunta: 29 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 07:47 GMT

Taron jam'iyar Republican

Jam'iyyar Republican a Amurka ta tsayar da Mitt Romney a matsayin dan takarar ta da zai kalubalanci Barack Obama a zaben shugaban kasar da za a yi a watan Nuwamba.

Wannan mataki ya bai wa Mista Romney damar yin amfani da kudaden da jam'iyyar ta tara don yakin neman zabe.

Da yake jawabi lokacin taron jam'iyyar a daren ranar Talata gwamnan jihar New Jersey, Chris Christie, ya ce Mista Romney zai yi jagoranci cikin adalci, kana ya bunkasa tattalin arziki da ma samar da ayyukan yi a kamfanoni masu zaman kansu.

Mai dakin Mista Romney, Ann Romney, ta jaddada asalinsu da halayya ga aiki wadda ta taimaka wa Mista Romney ya samu sa'a a harkokin kasuwanci.

Ta ce, "Ya yi kokarin tafiyar da rayuwarsa da yin aiki da wasu akidoji na kula da iyali da addini da kuma kauna ga sauran 'yan uwansa mutane. Ba zan iya gaya muku abin da zai faru ba nan da shekaru hudu masu zuwa, amma ina tsaye ne cikin wannan dare a matsayin mata, da uwa, da ma kaka 'yar Amurka. Kuma alkawarin da zan yi muku shi ne, wannan mutumin ba zai baku kunya ba.''

Shi ne zai iya fafatawa da Obama

'Yan jam'iyyar Republican dai sun amince cewa Mitt Romney ne mutumin da zai iya fafatawa da shugaba Obama a zaben shugaban kasar da za a gudanar a watan Nuwamba mai zuwa.

Sun ce irin jajircewar da ya yi a zaben fitar da dan takarar jam'iyyar shekarun hudu da suka gabata lokacin da, John McCain, ya yi nasarar yi wa jam'iyyar takara ya nuna cewa shi dan takara ne mai hakuri wanda zai iya jure wa kalubalen da Amurka ke fuskanta.

A ranar Alhamis Mista Romney zai gabatar da jawabi game da takararsa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.