BBC navigation

Adadin 'yan Syria da su ka tsere daga Kasar sun zarta hasashe

An sabunta: 28 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 17:02 GMT
Syria

Ana ci gaba da rikici a Syria

Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin 'yan kasar Syria da su ka tsere daga kasar sakamakon tashin hankalin dake faruwa, sun yi matukar zarta yadda aka yi hasashe

Majalisar dinkin duniyar ta kuma yi gargadin cewa hakan wata alama ce ta kwararar 'yan gudun hijira.

Wata mai magana da yawun Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar dinkin duniya, UNHCR, Melissa Fleming ta ce yawan mutanen dake shiga kasar Jordan daga Syria ya ninka cikin mako guda,

Ta kara da cewa 'yan gudun hijira kimanin dubu dari biyu da goma sha biyar ne aka yi wa rajista a kasashe hudu, da su ka hada da Jordan da Iraki, da Labanon da kuma Turkiyya masu makwabtaka da Syriar.

A halin da ake ciki, masu fafutuka a kasar ta Syria sun ce sojin kasar sun kaddamar da wasu sabbin hare hare a gabas da birnin Damascus.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.