BBC navigation

Kotu ta sami tsohuwar minista da laifi a kisan musulmi a Gujarat

An sabunta: 29 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 17:01 GMT
Wasu mata a Gujarat

An kashe musulmi da dama a Gujarat

Wata kotu a India ta samu wata tsohuwar ministar gwamnati da hannu a kisan kare dangin da aka yi wa wasu musulmi casa'in da biyar, a lokacin wani rikicin addini a jihar Gujarat, shekaru goma da su ka wuce.

Ana zargin Maya Kodnani ne da tunzura jama'a su afka wa al'umar Musulmi a birnin Ahmedabad.

An same ta da laifi ne tare da wani jagoran mayakan 'yan kishin Hindu, Babu Bajrangi, da wasu mutanen su talatin.

Tarzomar ta Gujarat ta barke ne bayan mutuwar wasu 'yan Hindu dake dawowa daga ziyarar ibada, a wata gobara da ta tashi a cikin jirgin kasa.

Mutane sama da dubu ne, galibinsu musulmi aka kashe, a hare haren ramuwar gayyar da su ka biyo baya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.