BBC navigation

Shugaban Senegal ya nemi a rusa majalisa

An sabunta: 29 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 10:24 GMT
Ambaliyar ruwa a Senegal

Ambaliyar ruwa a Senegal

Shugaban kasar Senegal Marky Sall ya nemi a rusa majalisar dattawan kasar, kuma a yi amfani da kudaden da zasu taru ta hakan, wajen taimakawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a kasar.

Shugaban ya katse ziyararsa zuwa kasar Afrika ta Kudu don fuskantar matsalar ambaliyar ruwa da ta yi sanadiyar mutuwar mutane 13.

Yayin da yake magana a filin jiragen sama na Dakar, Mista Sall ya ce zai gabatar da kudurin doka da za ta nemi rushe majalisar dattawan.

Kudaden da aka kebe don kashewa majalisar sun kai dalar Amurka miliyan 15, kuma za a yi amfani da kudaden wajen kare aukuwar ambaliyar ruwa a kasar.

Kodayake babban birnin kasar wato Dakar dake cikin kwari na fuskantar ambaliya a duk damuna, a wannan shekarar kasashen yammacin Afrika sun fuskanci ruwa kamar da bakin kwarya.

Rahotanni sun ce mazauna birnin da abin ya shafa sun yi zanga-zanga a titunan birnin domin nuna fushinsu da rashin daukar matakai a kan lokaci da suka ce gwamnatin ba ta yi ba.

Inda aka yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa su.

An ruwaito shugaban yana jaddada muhimmancin majalisar dattawan, amma kuma ya ce magance matsalar dake fuskantar al'ummarsa ya fi muhimmanci.

Ambaliyar ruwa a Senegal

Ambaliyar ruwa a Senegal

A watan Mayu ne dai Babban Bankin Duniya ya yi alkawarin baiwa Senegal sama da dala miliyan 55 don ta karfafa kariya daga aukuwar ambaliyar ruwa, musamman a wajen birnin na Dakar.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.